Kwarai, kun ji sarai. Ni da abokin aiki na @charlesinojie mun kaddamar da Make We Hala Challenge. Ku nuna cewa ku ma zaku daga murya ta hanyar yin naku bidiyon ko hoto tare da rubuta #MakeWeHala. Zan wallafa guda 10 da suka fi kyau, sannan wanda ya fi kyau zai samu Android phone mai kyau. Ku daga murya don tabbatar da cewa baza ku zama yan kallo in ku ka ga ana cin zarafin dan adam ba.